Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta dakatar da daukar Mata-Maza aikin soja

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da matakin haramta daukar mutanen da suka sauya halittan jinsinsu zuwa kowanne matsayi na aikin soja a kasar.Matakin da ke cikin jerin tsare-tsaren da tsohuwar Gwamnatin Barack Obama ke marawa baya.

shugaban kasar Amurka Donald Trump
shugaban kasar Amurka Donald Trump
Talla

Shugaba Donald Trump a sanarwar dakatarwar da ya fitar, ta ce bukatar da ake da ita shi ne ganin Sojin Amurka da karsashi da kuma kwarewa ba tarin rubabbun Dakarun da ka iya zamewa Gwamnati kaya ba.

Trump ya bayyana cewa bayan ya yi nazari tare da karbar shawarwari daga manyan janar-janar din soji da kuma masana harkokin soji sun tsaida shawara cewa Gwamnati ba zata amince da diban mutanen da suka sauya jinsin ba a aikin sojan kasar.

Sanarwar dai ta kasance tamkar an yi amai an lashe ne game da harkan sojin kasar da ke ta kokarin aiwatar da tsare-tsaren da tsohuwar Gwamnatin Obama ta bar masu na diban irin wadannan mutane.

Sarah Huckabee Sanders kakakin fadar shugaban Amurkan ta yi bayanin cewa matakin shugaban kasar ba wai da wata niyya ce daban ba illa iyaka ganin ana da dakaru masu iya aikin soji yadda ya kamata.

Babbar ayar tambaya kan wannan sanarwa ta shugaba Donald Trump ita ce, ko yaya kasar zata yi da dimbin wadanda tuni aka riga aka diba cikin aikin sojan Amurkan, alhali kuwa ana sane da sauyin halittar ta su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.