Isa ga babban shafi
Faransa

Ministar Tsaron Faransa ta yi murabus

Ministar Tsaron Faransa, Sylvie Goulard ta yi musarabus sakamakon wata badakalar ayyukan boge da ta kunno kai a Jam’iyyarta ta MoDem mai kawance da Jam’iyyar shugaba Emmanuel Macron.

Ministar Tsaron Faransa mai murabus Uwargida Sylvie Goulard
Ministar Tsaron Faransa mai murabus Uwargida Sylvie Goulard REUTERS/Bertrand Guay/Pool
Talla

Uwargida Sylvie Goulard ta ce, ba za ta ci gaba da rike mukamin gwamnati ba a dai dai lokacin da alamu ke nuna cewa, akwai yiwuwar ta fuskanci tuhuma bisa zargin barnatar da kudade a lokacin da ta ke mamba a Majalisar Dokokin Tarayyar Turai.

Goulard ta yi murabus ne a yayin da shugaba Emmanuel Macron ya yi kwarya-kwaryan garanbawul a gwamnatinsa bayan zaben ‘yan Majalisar Dokokin kasar da aka gudanar a karshen makon, in da ya jam’iyyarsa da kawarta ta MoDem suka samu gagarumin rinjaye.

Kimanin wata guda kenan da aka nada Goulard a matsayin Minister Tsaron Faransa bayan Macron ya lashe zaben shugaban kasa.

A cewar Goulard, shugaba Macron na kokarin dawo da martabar gwamnati a idon jama’ar Faransa da nahiyar Turai, saboda haka dole ne ta dauki matakin kawar da duk abin da ka iya kawo wa gwamnatinsa cikas.

Wannan ne ya sa ta bukaci shugaba Macron da ya ba ta damar yin murabus.

A cikin wannan watan ne, masu shigar da kara a birnin Paris suka fara gudanar da bincike bisa zargin cewa, Jam’iyyar MoDem ta yi amfani da kudaden Majalisar Dokokin kasashen Turai wajen biyan kananan ma’aikatanta a Faransa.

Sai dai shugaban Jam’iyyar ta MoDem Francois Bayrou ya musanta zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.