Isa ga babban shafi
Faransa

Fillon na fuskantar sabon zargi

Yayinda ya rage kasa da watanni uku, a gudanar da zaben shugabancin kasar Faransa, jaridar Canard Enchainé, ta sake bankado wani sabon zargi da ake wa matar dan takarar shugabancin kasar, a jam’iyar Republican François Fillon.

Dan takarar shugabancin Faransa François Fillon da matarsa Penelope Fillon
Dan takarar shugabancin Faransa François Fillon da matarsa Penelope Fillon REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Jaridar ta gano sau biyu maidakin Fillon tana karbar euro 45,000 a matsayin kudaden sallama daga majalisar dokokin ta Faransa.

Wannan dai na zuwa a yayinda Fillon ke kokarin kubutar da kansa daga zargin baiwa matarasa aikin bogin da ya bata damar amfana da albashin euro 5,000 tsawon shekaratu 4 daga shekarar 1998 zuwa 2002.

Wata sabuwar da jaridar ta canard enchainé ta gano cewa matar tsahon Firaministan Faransar, Penelope Fillon ta karbi wasu kudade da yawansu yakai euro dubu 16 a 2002, da kuma wasu euro 29,000 a shekarar 2013 a matsayin kudaden sallamar aiki daga majalisar dokoki.

Tuni dai dan takarar na jam`iyyar Republican, François Fillon, ya mayar da martani, inda ya danganta ikirarin na canard enchainé da zama karya tsagoronta, da kuma ke tattare da kuskure.

Fillon ya musunta karbar euro 29,000 da jaridar tace matar ta yi a watan Nuwamba, a shekara ta 2013 da cewa euro 7,754 ne, da suka hada da kudaden hutu, inda ya ce jaridar ta yi kuskure wajen hadawa da euro 29,000 da aka baiwa matarsa a watan ogustan 2007, bayan da ta share shekaru 5 tana mai taimakawa Marc Joulaud mataimakin da ya maye gurbin Fillon a kujerar majalisar dokokin kasar ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.