Isa ga babban shafi
Faransa

Fillon ya gamu da sabbin zarge-zarge a Faransa

Wasu sabbin rahotanni na cewa dan takarar shugabancin Faransa karkashin jamiyyar Conservative Francois Fillon ya samawa matarsa da ‘ya’yan sa biyu ayyuka da suke samun kudin Turai kusan Euro miliyan daya.

Francois Fillon da matarsa Pénélope Fillon a birnin Paris na Faransa
Francois Fillon da matarsa Pénélope Fillon a birnin Paris na Faransa REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Wata jaridar Faransa mai suna Canard Enchaine ce ta yi wannan sabon rahoto da aka wallafa.

Sabon rahoton da jaridar ta fitar na cewa uwargidan dan takarar Penelope, na karbar  Euro dubu 900 a matsayin sakatariyar mijinta, yayin da biyu daga cikin ‘yan’yanta biyar ke karban albashin da ya kai Euro dubu 84 a matsayin masu taimakawa mahaifin nasu.

Francois Fillon dai na sahun gaba cikin wadanda ake zaton za su iya samun nasarar hawa kujerar shugabancin Faransa, amma kuma sakamakon wadannan zarge-zarge ana ganin cewa farin jininsa ya ragu ainun tun fara tonon sililin da aka fara yi masa makon jiya game da zargin matarsa da diban miliyoyin kudade, ba tare da sanin takamaiman aikin da ta ke yi ba.

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewar, yanzu haka Marine Le Pen mai kyamar baki ke sahun gaba wajen lashe zaben da za a gudanar a watan Mayu mai zuwa, sai kuma Fillon da Emmanuel Macron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.