Isa ga babban shafi
Amurka-Jamus

Obama ya kamalla ziyararsa ta karshe a Turai

Shugaba Barack Obama da ke rangadin bankwana a Turai ya yaba da hadin kan da ke tsakanin Amurka da Jamus karkashin Shugabar gwamnati Uwargida Angela Merkel tare da fatan zumuncin zai dore da wanda zai gaje shi.

Obama da uwargida Angela Merkel ta jamus a ziyararsa ta karshe a Turai.
Obama da uwargida Angela Merkel ta jamus a ziyararsa ta karshe a Turai. REUTERS/Fabrizio Bensch
Talla

Shugaban Amurkan mai barin gado Barack Obama ya yi fatan wanda zai gaje shi Donald Trump zai dauki darasi wajen sanin wuraren da suka dace su yi zumunci da Rasha.

Kalaman Barack Obama game da Rasha sun kasance karon farko tun yakin neman zaben Donald Trump inda aka yi ta fadin cewa Rasha na da hannu wajen satar wasikun sirrin uwargida Hillary Clinton  wacce ta tsaya takara da Trump saboda dangantaka da ke tsakanin Trump da shugaba Vladmir Putin.

A na ta jawabin Uwargida Angela Merkel ta yi nuni da cewa yarjeniyoyi na ciniki tsakanin kungiyar kasashen Turai da Amurka ba zai yiwu su karkare ba saboda ganin shi sabon shugaban Amurka mai jiran gado na adawa da yarjeniyoyin.

Uwargida Angela Merkel ta kuma nuna gamsuwa da yadda Amurka ke tafiyar da mika mulkin tsakanin shugaba mai barin gado da wanda yake jiran gado wanda acewarta ya bada karfin gwiwa na dorewar dasawa tsakanin kasashen
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.