Isa ga babban shafi
Jamus-Afrika

Jamus na daf da karfafa tattalin arzikin Nahiyar Afrika

Gwamnatin Jamus ta bukaci kasashen da suka cigaba, su marawa shirinta baya na karfafa tattalin arzikin kasashen nahiyar Africa, samar da ayyukan yi, da kuma rage kwararar ’yan gudun hijira zuwa nahiyar Turai.

Sugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Sugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel. © REUTERS/Fabrizio Bensch
Talla

Mai Magana da yawun Gwamnatin Jamus, Gerd Mueller, ya ce nan da ‘yan makwanni, kasar zata fitar da cikakkun bayanan tsarin da ta yiwa taken “Marshall Plan For Africa”.

A baya kasar Amurka ta taba amfani da makamancin tsarin, wajen tallafawa tattalin arzikin Jamus da ya durkushe, bayan kammala yakin Duniya na biyu.

A satin da ya gabata, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya, IOM, ta ce akalla masu gudun hijira 160,000 ne suka ketara zuwa nahiyar Turai daga Africa, yayinda 4,220 suka mutu a kokarin ketara tekun Meditterranian zuwa nahiyar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.