Isa ga babban shafi
Hungary

Bazamu amince da tilastawa ba daga Tarayyar Turai-Hungary

Firaministan Hungary Viktor Orban yace kungiyar kasashen Turai ba zata tilasatawa kasarsa karbar baki yan kasashen waje ba kamar yadda ta shatawa duk wata kasa dake cikin ta adadin bakin da zata karba.

Wasu 'yan gudun hijira da ke kan iyakar kasar Hungary da Slovenia
Wasu 'yan gudun hijira da ke kan iyakar kasar Hungary da Slovenia REUTERS/Srdjan Zivulovic
Talla

A zaben raba gardamar da aka gudanar a kasar, dan adawa da shirin karbar bakin, kashi sama da 99 sun goyi bayan shirin kin karbar bakin, sai dai addain mutanen da suka shiga zaben bai kai kashi 50 na masu rajistar zabe ba, wato miliyan 3,300,000 daga cikin miliyan 8.

Wannan ya sa shugabanin yan adawar kasar suka bukaci Orban mai tsananin kiyayar baki ya sauka daga kujerar sa.

A baya dai wasu sun sha kira ga Tarayyar Turai ta dauki tasttsauran mataki kasar Hungary saboda matakin mahukuntar kasar nakin baki ‘yan gudun hijira.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.