Isa ga babban shafi
Morocco

Za'a kwashe 'yan Morocco da ke zaune a Jamus ba bisa ka'ida ba

Hukumomin kasar Morocco sun amince sun kwashe ‘yan asalin kasar da ke zaune Jamus ba bisa ka’ida ba domin dawo da su gida.

Talla

Sarkin Morocco Mohammad na shida ya tattauna kan wannan batu da waziriyar kasar ta Jamus Angle Merkel ta wayar tarho ranar larabar da ta gabata kan wannan shiri na kwashe ‘yan daga Jamus.

Markel tana fuskantar matsin lamba kan kawo karshen kwarar ‘yan gudun hijira cikin kasar ba bisa ka’ida ba, wanda yawansu yak ai kimanin miliyan daya a shekarar da ta gabata.

A kwanakin da suka gabata an kama a kalla ‘ayn gudun hijira 70, bayan aikata ko kuma yunkurin aikata fyade da suke yi a Jamus, kuma duka ‘yan kasar ta Morocco.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.