Rudani a filin saukar jiragen saman John F Kennedy da ke New York
Dimbin fasinjoji ne aka kwashe tare da dakatar da tashin jirage a wani sashe na filin saukar jiragen saman John F Kennedy da ke birnin New York sakamakon yada wata jita-jita da ke cewa an ji karar harbe-harbe a filin jiragen saman.
Wallafawa ranar:
Bayan kammala bincike, shugaban rundunar ‘yan sandan musamman a birnin na New York Harry Wedin, ya ce ba su gano komai ba, kuma ga alama bayanan na jita-jita ne.
Amurka ta dauki tsauraran matakan tsaro don hana aukuwar harin ta'addanci ganin yadda aka yi ta samun wasu hare-haren da ake dangatawa da ayyukan masu tsautsauran ra'ayin addini, a bana an kai hare-haren ta'addanci a wasu jihohin kasar inda aka sami asarar rayukan mutane da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu