Isa ga babban shafi
Faransa

Al'ummar Nice sun yi wa Valls ihu

Al’ummar birnin Nice na Faransa da aka kashe wa mutane 84 a harin da aka kai ranar yancin kasar sun yi wa Firaminsitan kasar Manuel Valls ihu bayan tsayuwar karrama mamatan. 

Al'ummar Faransa sun yi tsayuwar karrama mamatan da suka rasu a harin Nice ranar jumma'a
Al'ummar Faransa sun yi tsayuwar karrama mamatan da suka rasu a harin Nice ranar jumma'a REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Wasu daga cikin mutanen sun dinga yi wa Firaministan tare da ministoci guda biyu ihu,  suna kiran su "makisa" da kuma kiran su sauka daga mukaman su sakamakon kisan.

A bangare daya, babban mai gabatar da kara a Faransa Francois Mollins ya bayyana cewar harin da aka kai birnin Nice na kama da wanda aka shirya shi.

Bincike ya nuna cewar wanda ya kai harin Mohammed Lahouaej Bouhel ya dade yana zagaya dandalin yana daukar hotan kan sa, kafin ya kai harin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.