EU za ta rika musayar bayanan fasinjoji
Majalisar Tarayyar Turai ta amince da wani mataki na musayar bayanan fasinjojin Jirgin sama tsakanin mambobin kungiyar wanda zai taimaka wajen tantance ‘yan ta’adda.
Wallafawa ranar:
Kudirin ya samu amincewar Majalisar ta Turai a yau Alhamis bayan shafe lokaci mai tsawo ana tabka muhawara a Strasbourg.
Tun a shekarar 2011 ne shugabannin kasashen kungiyar Turai 28 suka gabatar da bukatar amma sai a yau bayan shafe shekaru 5 aka amince da matakin wanda zai taimaka ga tantance ‘yan ta’adda musamman sakamakon hare hare ta’addanci da aka kai a biranen Paris na Faransa da Brussels na Belgium.
Yan majalisar 416 ne suka amince da matakin yayin da 179 suka kada kuri’ar kin amincewa, wasu tara kuma suka kaurace.
A cikin sanarwar da ta fitar, hukumar tarayyar Turai ta ce, wannan ya nuna kasshen Turai a shirye suke tare da hadaka kai wajen yakar ta’addanci.
Maharan da suka kai hari a tashar jirgin sama a Brussels dukkaninsu sun shigo Turai ne ta jirgin sama daga Turkiya ba tare da an gane su ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu