Isa ga babban shafi
Girka

Alexis Tsipras ya yi Murabus daga mukamin sa

Firaministan kasar Girka Alexis Tsipras ya ajiye mukaminsa tare da kiran a gudanar da zaben gaggauwa domin kawo karshe rikicin siyasar kasar.

Firaministan Girka Alexis Tsipras.
Firaministan Girka Alexis Tsipras. REUTERS/Christian Hartmann
Talla

A wani jawabi da ya gabatar dazu-dazuna Tsipras ya ce zai gana da shugaban kasar domin gabatar da takardarsa ta murabus da kuma majalisar ministocinsa.

Wata majiya na cewa abu ne mai yiyuwa a gudanar da zaben gaggawar a ranar 20 ga watan satumba mai zuwa.

Sanar da ajiye Mukamin  Tsipras na zuwa ne bayan Girka ta biya bankin turai bashin sama euro biliyan uku da rabi daga cikin bashin da aka ba ta da ya kai euro bilyan 23.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.