Isa ga babban shafi
Netherlands

Karancin masu laifi ya sa ana rufe gidajen Yari a Netherlands

Rahotanni daga kasar Netherlands na cewa Hukumomin kasar sun fara rufe gidajen yari a sassan kasar sakamakon karancin ma su aikata laifuka da ake samu. A tashin farko Gwamnatin kasar ta rufe gidajen yari kimanin takwas.

Netherlands ta fara rufe gidajen yari a sassan kasar sakamakon karancin ma su aikata laifuka da ake samu.
Netherlands ta fara rufe gidajen yari a sassan kasar sakamakon karancin ma su aikata laifuka da ake samu. Amnesty.fr
Talla

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun cunkoson a gidajen yari a kasashe da daman a duniya.

Ma’aikatar shari’a da ke kasar ta fadi cewa ta dauki dukkan matakan da suka dace domin ganin an rufe gidajen yarin saboda ba a samun mutanen da za a zuba a ciki.

Bayanai na cewa duk da c kasar na da gidajen yari da zai kunshi mutane dubu 14 sai gashi ana karancin samun masu lafiyin da za su kargame

Mukaddashin Ministan shari’a na kasar ya fadi cewa suna ganin nan gaba dole a kara rufe wasu wuraren tsare mutanen saboda karancin masu laifi.

Wani rahoto a bara na nuna cewa cunkoson da ake samu a gidajen yari da ke wasu kasashen duniya, na daga cikin abubuwan da ke hana rufe gidajen yarin da ake da su.

Kungiyoyi daban daban a kasar sun nemi Gwamnatin kasar kada ayi bankwana da gidajen sarka, abar kadan da za a rika ajiye wadanda ya zama dole.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.