Isa ga babban shafi
EU-FARANSA-ALLEMAGNE

Faransa da Jamus na zaman taro a kan batun biyan bashin kasar Girka

Shuwagabanni Kasashen Faransa da Jamus, sun amince su cigaba da tattaunawa kan dimbin bashin da ake bin Girka duk da yake babu wani cigaba da ake samu. Bayan sun kwashe daren jiya suna tattaunawa tsakanin shuagba Francois Hollande, Angela merkel da Alexis Tsipiras, shugabanin sun yi alkawrin dinkin barakar dake tsakanin su.

waziriyar Jamus Angela Merkel, da Shugaban gwamnatin Girka, Alexis Tsipras da François Hollande na faransa sun tattauna
waziriyar Jamus Angela Merkel, da Shugaban gwamnatin Girka, Alexis Tsipras da François Hollande na faransa sun tattauna REUTERS/Yves Herman
Talla

Bayan sun kwashe daren jiya suna tattaunawa tsakanin shuagba Francois Hollande, Angela merkel da Alexis Tsipiras, shugabanin sun yi alkawrin dinkin barakar dake tsakanin su, kafin Hukumar Bada lamuni ta Duniya da kungiyar kasashen Turai su sake baiwa kasar rancen sama da Dala biliyan 7.

Girka na fuskantar matsala wajen biyan euro biliyan daya da rabi nan da karshen wanan wata.

Ita dai gwamnatin kasar Girka taki amincewa da tsarin da masu bata bashin suka gabatar, a yayinda ta gabatar da nata wanda tace shine kan adalci, idan dai babu wata mafita a tsakanin bangarorin biyu ana fuskantar barazanar ficewar kasar daga cikin jerin kasashen dake amfani da kudaden Euro a nahiyar turai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.