Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta nuna adawa kan batun bakin haure

Faransa ta ce ba ta goyon bayan shawarwarar da wasu kasashen Turai suka bayar, da ke neman a raba wa kasashen Nahiyar dawainiyar bakin hauren da shiga yankin.Manuel Valls Firaministan Faransa wanda ke jawabi a lokacin da ya ziyarci yankin Menton da ke kusa da iyakar kasar da Italiya, ya ce Faransa na adawa da duk wani mataki na rabawa kasashen Turai bakin hauren da ke shiga yankin, inda ya ce Faransa ba ta taba goyon bayan irin wannan shawara ba.

Fira Minista Manuel Valls yayin ziyarar da ya kai a Menton
Fira Minista Manuel Valls yayin ziyarar da ya kai a Menton REUTERS/Jean-Christophe Magnenet/Pool
Talla

Valls ya furta hakan ne a wannan yanki da ke kunshe da bakin haure mafi yawan su daga Nahiyar Afirka ke zaune a wani sansani bayan kama su a kokarinsu na shiga nahiyar Turai ta hanyar amfani da kwale-kwale.

A ranar laraba ta makon jiya ne kungiyar ta Tarayyar Turai ta gabatar da wannan shiri da ke neman a rabawa kasashen yankin bakin haure a maimakon barin dawainiyar su a wuyan kasashen da suka kama su, kuma kawo yanzu kashi 75 cikin dari na bakin hauren da suka shiga Turai na zaune ne a kasashen Faransa, Italia, Jamus, Birtaniya da kuma Sweden.

Shi ma dai tsohon shugaban kasar ta Faransa Nicolas Sarkozy ya ce ba ya goyon bayan wannan shiri na kungiyar tarayyar Turai.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.