Isa ga babban shafi
Girka

Girka da kasashen Turai na gudanar da taro kan tattalin arziki

Yau ake gudanar da taro tsakanin kasar Girka da sauran kasashen kungiyar tarayyar Turai ta EU a birnin Brussels, inda ake tunanin Firaiminista Alexis Tsipras zai roki takwarorinsa, su bai wa kasar karin kudaden da za a ceto ta daga matsalar tattalin arziki

Le président du Parlement européen Martin Schulz lors d'une conférence de presse donnée à Pékin, à propos de la Banque asiatique d'investissement pour les infrastructures, le 17 mars 2015.
Le président du Parlement européen Martin Schulz lors d'une conférence de presse donnée à Pékin, à propos de la Banque asiatique d'investissement pour les infrastructures, le 17 mars 2015. REUTERS/Kim Kyung-Hoon
Talla

Duk da cewa kasar ta Girka bata cikin ajandar taron na yau ba, wani babban jami’in kungiyar tarayyar Turai ta EU ya ce za a tattauna batun kasar ne saboda fargabar da shugabannin kungiyar mai membobi 28 ke yi, na yiyuwar ficewa kasar daga tarayyar Turai.

Shugabar gwamnatin jamus Uwar gida Angela Merkel, ta shaida wa majalisar dokokin kasar cewa bai kamata su dami kansu ba, akan lamarin kasar ta Girka ba.

Sai dai Merkel, da kasar ta ce, ta fi kowace karfin tattalin arziki tsakanin kasashen na Turai, ta kau da yiyuwar ficewar Girkan daga jerin kasashen da ke amfani da kudin Euro.

Firaiministan kasar ta Girka ne ya nemin shugaban kungiyar EU Donald Tusk ya gana da shi, da shugabar gwammantin Jamus Angela Markel da kuma Shugaban Faransa Francois Hollande kan wannan lamarin.

Shi ma dai shugaban hukumar taraiyyar Turai Jean-Claude Juncker, zai halarci taron tare da shugaban babban bankin Turai Mario Draghi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.