Isa ga babban shafi
Vanuatu

Kayayyakin jin kai sun fara sauka Vanuatu bayan aukuwar bala'i

An fara samun saukar kayan agaji a tsibirin Vanuatu, da ya gamu da bala’in iska da ruwan sama a karshen mako, sai dai kamar yadda rahotanni ke cewa akwai wasu bangarori a cikin kasar da al’umma ke cikin matsanancin hali na rayuwa

Wasu daga cikin gidajen da iskar ta rusa
Wasu daga cikin gidajen da iskar ta rusa Reuters/Dave Hunt/Pool
Talla

Kungiyar bayar da agaji ta Oxfam tare da kasar New Zealand, sun isar da kayayyakin agajin gaggawan, duk da koma bayan da kungiyoyi ke fuskanta na rashin hanyoyin mota wajen isar da agajin, yayinda kuma, akwai wasu sassa na kasar da jami’an agajin suka kasa kai dauki, sakamakon rashin hanyoyi.

A wani hoton tauraron dan adam, ya nuno jama’ar yankunan Ambryn da Tongoa na bayyana bukatunsu a rubuce, ganin babu hanyoyin da taimakon zai kai garesu,

Ana sa ran samun karin agaji daga wasu kasashen duniya da katafaren kamfanin nan mai samar da man kwakwa na COPSL ya dauki nauyin saukewa.

Tsibirin Vanuatu dake kudancin tekun Pacific, ya fuskanci mahaukaciyar Guguwar ne a ranar jumma’ar data gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.