Isa ga babban shafi
Jamus

An yi bikin tunawa da ballewar bangon Berlin

A kasar Jamus an gudanar da bikin cika shekaru 25 da tunawa da ballewar bangon Barlin. Bikin kuma ya samu halartar dimbim mutane da dama.A lokacin da ta ke jawabi shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi jinjiina ga jamusawan da suka balle bangon, wanda kuma aka bayyana ya yi sanadin kawo karshen yakin cacar-baka a duniya.

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da Jamusawa suna manna faranni a bangon Berlin
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da Jamusawa suna manna faranni a bangon Berlin REUTERS/Fabrizio Bensch
Talla

Merkel ta ziyarci inda aka kashe mutane 138 a Berlin lokacin da suke kokarin tserewa daga bangaren da ke amintaka da tsohuwar daular Soviet.

A shekara ta 1961 ne aka gina bangon Barlin domin haramtawa mutane tserewa zuwa yammaci daga yankin gabaci masu ra’ayin gurguzu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.