Isa ga babban shafi
Faransa

Valls ya yi wa gwamnatinsa garanbawul

Babban sakatare a fadar shaugaban kasa ta Elysee Jean-Pierre Jouyet ne ya sanar da sunayen mambobin sabuwar gwamnatin Faransa da ke dauke da sabbin fuskoki uku bayan shugaban kasar ya umurci Firaminista Manuel Valls da ya yi wa gwamnatinsa garambawul.

Shugaban Faransa François Hollande tare da Firaminista Manuel Valls.
Shugaban Faransa François Hollande tare da Firaminista Manuel Valls. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Sabbin Ministocin sun da na kudi kudi Emmanuel Macron wani na hannun damar shugaba Francois Hollande da kuma Patricek Kanner da aka nada a matsayin ministan matasa da wasanni.

Ko baya ga mukamin manyan sakatarori ko kananan Ministoci a ma’aikatun gwamnati da ka bai wa wasu mata, haka zalika akwai 8 da aka nada a matsayin cikakkun Ministoci.

Sabon Ministan kudin mai shekaru 36 a duniya Emmanuel Macron, ya kasance mataimakin babban sakatare a fadar shugaban kasar sannan kuma mai bai wa shugaba Hollande shawara kan lamurran da suka shafi tattalin arziki.

Shugaba Francois Hollande dai ya umurci Firaminsita Manuel Valls da ya yi wa gwamnatinsa garambawul ne, bayan da wasu ministoci uku ciki har da na tattalin arziki Arnaud Montebourg suka fito fili suka soki salon siyasarsa ta tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.