Le Pen zata jagoranci adawa a Turai
Bayan kammala zaben majalisar kasar Turai , Shugabar Jamiyyar National Front a kasar Faransa Marine Le Pen tace tana da kyakyawan burin ganin ta hada kan masu ra’ayinsu a majalisar.
Wallafawa ranar:
Bayan nasarar samun kashi 25% na kuri’u daga kasar Faransa, Marine Le Pen ta bayyana gaban manema labarai a Brussels tare da masu ra’ayi daya daga kasashe hudu. Le Pen ta bayyana cewa sun damu matuka game da ci gaban kungiyar Turai a nan gaba.
Idan dai aka amince da kungiyar su a majalisar ta Turai, bangarorin masu ra’ayin kishin kasa za su yi nasarar gabatar da ra’ayinsu a majalisar ba tare da jibin goshi ba, kuma suna iya rike shugabancin kwamiti daga cikin kwamitoci 20 na majalisar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu