Isa ga babban shafi
Kungiyar Tarayyar Turai

An fara zaben Majalisar Dokokin Tarayyar Turai

A yau alhamis ne aka soma gudanar da zaben ‘yan Majalisar Dokokin Kungiyar Tarayyar Turai, inda mutane fiye da milyan 380 ke jefa kuri’a domin zaben wakilai 751 da za su wakilce su a wannan Majalisa.

Zauren Majalisar Tarayyar Turai, Strasbourg, Faransa.
Zauren Majalisar Tarayyar Turai, Strasbourg, Faransa. Reuters/Vincent Kessler
Talla

An dai soma zaben ne a kasashen Birtaniya da kuma Netherlands kafin sauran kasashen na Turai 28 su ci gaba da gudanar da nasu zaben.

To sai dai rahotanni na nuni da cewa za a sami karancin fitowar jama’ar da za su jefa kuri’a a wannan zabe, musamman ma masu adawa da ci gaba wanzuwar wannan kungiya.

A zaben da aka gudanar shekara ta 2009, kashi 43 cikin dari na al’ummomin kasashen ne suka fito zaben.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.