Isa ga babban shafi
Turkiya

An dakile Twitter a Turkiya

Masu mu’amula da shafin Twitter sun ruwaito cewa an dakile shafin bayan barazanar rufe shafin da Firaminista Recep Tayyip Erdogan ya yi da sauran dandalaye da ake yada bayanai game da badakalar cin hanci da Rashawa da suka dabaibaiye gwamnatinsa.

Friministan Turkiya  Recep Tayyip Erdogan
Friministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Umit Bektas
Talla

Amma kamfanin dillacin labarai na Anatolia mallakar gwamnatin Turkiya yace mahukunta sun dakile Twitter ne saboda kin bin wasu umurnin kotu akan cire wasu shafuka da gwamnatin tace sun saba mata.

Wannan matakin ya biyo bayan barazanar da Erdogan ya yi na rufe Twitter a Turkiya a wani gangamin siyasa na yakin neman zaben kananan hukumomi da za’a gudanar a ranar 30 ga watan Maris.

Akwai wasu zantukan Erdogan da ake yadawa a shafukan Intanet da suka shafi cin hanci da rashawa da suka dabaibaye shi.

Baya ga Twitter, Erdogan ya sha alwashin rufe YouTube da Facebook da ‘Yan adawa suka fake suna caccakar gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.