Isa ga babban shafi
Faransa

Faransawa sun soki dokar halatta zubar da ciki

Da dama daga cikin al’ummar kasar Faransa sun nuna rashin amincewar su da wata doka da majalisar dokokin kasar ke son aiwatarwa da zai bai wa mata izinin zubar da ciki a duk lokacin da suke bukata.

Wasu takardun da ke dauke da bayanan adawa da zubar da ciki a Faransa
Wasu takardun da ke dauke da bayanan adawa da zubar da ciki a Faransa celesteh/Flickr/CC
Talla

Dubban mutane a kasar ne suka nuna rashin amincewarsu da dokar da zata bai wa mata damar zubar zubar da ciki.

Rahotannin sun bayyana cewa mutanen da suka halarci zanga zangar da aka gudanar domin nuna kyamatar dokar a ranar Talata sun kai 40,000.

A ranar litanin mai zuwa ne ‘yan Majalisar dokokin Faransa zasu fara tafka mahawara akan batun na yiyuwar bai wa mata damar zubar da cikin, idan ci gaba da rike cikin na iya yi wa koshin lafiyarsu ko ta jaririn illa.

Haka kuma dokar ta tanadi hukunta duk wanda yaki bai wa matan masu son zubar da cikin gudunmuwa wajen aiwatar da zubar da cikin idan yana da masaniya akan haka.

Alkaluma sun nuna cewa a Kasar Faransa akalla ana zubar da ciki Dubu Dari da Ashirin a duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.