Isa ga babban shafi
Italiya

An ci gaba da sauraran shari'ar matukin jirgin ruwan Concordia

Matukin jirgin ruwan mai suna Francisco Schettino na fuskantar dauri ne na tsawon shekaru 20 saboda ganganci daya kai ga mutuwar mutane da yawa dake cikin jirgin sa a gaban ruwan tsubirin Giglio.

Jirgin ruwan Coata Concordia a lokacin da ya yi hatsari
Jirgin ruwan Coata Concordia a lokacin da ya yi hatsari
Talla

Lauyoyin dake wakiltan wasu mamatan sun fadawa manema labarai cewa suna bukatar adalci a wannan sharia, domin hatta wadanda suka tsira daga wancan hatsari zasu dade suna mafarkin abin.

A makon jiya aka fara sauraron waccan sharia, amma kuma aka dakatar saboda yajin aikin da lauyoyi suka shiga .

Shi jirgin ruwan dai ya sami matsala ne a gaban ruwan Giglio a daren ranar 13 ga watan Janairu na bara, yana dauke da mutane samada 4, 200 daga kasashe 70 na duniya, kuma jimillan mutane 32 suka mutu.
Matukin jirgin ruwan Francisco Schettino, 52 ya sha suka domin ana ganin laifin matunne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.