Isa ga babban shafi

Amurka tana Fuskantar suka daga kasashen Turai akan leken asirinsu

Shugaban Faransa Francois Hollande ya bukaci Amurka ta gaggauta jingine leken asirin da ta ke wa kasashen Turai tare da gargadin hakan na iya gurgunta huldar kasuwancinsu, bayan wani rahoto da aka fitar wanda ke zargin Amurka tana leken asirin ayyukan diflomasiyar kasashen Turai.

Shugaban Faransa, Francois Hollande.
Shugaban Faransa, Francois Hollande. EUTERS/Francois Lenoir
Talla

“Ba za mu amince da wannan tabi’ar ba tsakanin abokan huldar mu” inji shugaba Hollande a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a wata ziyara da ya kai a Lorient.

Shugaban ya kara da cewa bayanan da suka tattara ya zama dole su bukaci karin bayani daga Amurka akan zargin leken asirin.

Tuni dai kungiyar Tarayyar Turai da Faransa da Jamus suka bukaci cikakken bayani daga Amurka akan leken asirinsu.

Kodayake sakataren harakokin wajen Amurka jonh Kerry wanda ke ziyara a kasashen Gabas ta tsakiya yace basu da masaniya akan leken Asirin Turai da jami’an leken asirin Amurka ke yi.

Wata Mujallar kasar Jamus ce dai ta buga labarin a ranar Lahadi, wanda ta danganta shi da tsohon jami’in leken asirin Amurka Edward Snowden inda mujullar ta ruwaito cewa Amurka na dasa na’urorin daukan bayanai a ofisoshin kungiyar kasashen Turai da ke birnin Washington.

Wata mai magana a madadin kungiyar Tarayyarar Turai, Viviane Reding ta ce wannan zargi da ake wa Amurka kan iya kawo cikas ga huldar da kasashen Turai da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.