Isa ga babban shafi
Sweden

Kura ta kwanta bayan share mako daya ana tarzoma a Sweden

Kura ta soma lafawa a tsakiyar ranar yau, bayan share kusan mako daya ana bata-kashi tsakanin ‘yan sanda da kuma matasa marasa aikin yi da ke gudanar da zanga-zangar a wasu unguwanni da ke birnin Stockholm fadar gwamnatin kasar Sweden.

Barnar da masu zanga-zanga suka yi a kasar Sweden.
Barnar da masu zanga-zanga suka yi a kasar Sweden. REUTERS /Fredrik Sandberg
Talla

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandar birnin na Stockholm Karin Solberg, ta ce an samu nasarar kwantar da tarzomar ne sakamakon irin gudunmuwar da kungiyoyin sa-kai da kuma iyayen yara suka bayar wajen kare unguwanninsu daga masu zanga-zangar.
A tsawon kwanakin da suka gabata, motoci da kuma shaguna masu tarin yawa ne aka kona musamman ma a unugwannin da ke wajen birnin inda ake da dimbin bakin haure, wadanda ke nuna bacin ransu dangane da rashin aikin yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.