Isa ga babban shafi
syprus

Kasar Syprus ba zata sake samun karin lamunin gyara komadar tattalin arziki ba.

Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel, tace ba za’a baiwa kasar Cyprus karin lamuni ba, bayan da ta nemi karin tallafin kudi na Euro Billion 17.

Shugabar gwamnatin kasar Jamus Uwar gida Angela Markel tana jawabi
Shugabar gwamnatin kasar Jamus Uwar gida Angela Markel tana jawabi
Talla

Da take jawabi shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Markel ta bayyana cewar yanzu sun cimma matsaya cewar abu ne mai mihimanci su hana Cyprus neman karin wani wa’adi, bayaga wanda aka diba mata tare da takwarorin ta na nahiyar Turai.

Tace “da-sannu muna nan muna biyar ka’idojin nahiyar mu ta Turai, kuma mun kusa kamma dukkanin yarjejeniyoyin da aka rattabawa hannu”

A ranar Alhamis dai ne ake tsammanin Ministan harkokin kudaden kasar Cyprus zai gana da jami’an Diplomasiyyar kungiyar tarayyar Turai domin fito da wasu sharuddan gyara komadar tattalin arziki kasar da bata da girma.

Kasar Cyprus dai na fatar samun bashin Euro Billion 5.0 daga kasar Russia kari ga Euro Billion 2.5 data Araa a shekarar 2011, amma kuma ba’a kammala shirin ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.