Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta yi Allah wadai da tilasatawan da akawa Diarra ya yi murabus

Kasar Faransa ta yi Allah wadai da tilastawan da akawa Firaministan kasar Mali, Cheick Modibbo Diarra, ya yi murabus, inda ta ce yin hakan na nuna akwai bukatar a tura dakaru zuwa kasar. Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Faransa ce ta ya yi kakkausan suka akan murabus din da aka Tilasta Firaminista Cheick Modibbo Diarra ya yi, inda mai Magana da yawun Ma’aikatar, Philippe Lalliot, ya kuma yi kira da Sojin kasar da su dai na tsunduma bakinsu a cikin harkar siyasar kasar. 

Shugaban kasar Faransa, François Hollande
Shugaban kasar Faransa, François Hollande REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Lalliot har ila yau ya yi kira da a kafa gwamantin mai wakilai a gurguje, ya kuma kara da cewa, tilastawa Firaministan da aka yi ya yi murabus na nuna akawi bukatar a tura dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar.

Wannan murabus da Diarra ya yi, ta z one jim kadan bayan shugaban sojin da suka yi juyin mulki a kasar, Kyaftin Amadou Sanogo ya bada odar a cafke Firaministan.

Shi dai Diarra na goyon bayan tura dakarun hadin gwiwa na Yammacin Afrika, domin su kwato Arewacin kasar dake hanun ‘Yan tawaye, sai dai baya goyon bayan tura Dakarun kasashen waje zuwa Malin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.