Mutumin da aka samu da laifin satar bayanai a fadar Paparoma ya daukaka kara
Wani mai kula da na’urorin komputa a fadar Paparoma, da aka samu da laifin tallafa wa mai kula da ma’aikatan fadar wajen satar bayanai, ya daukaka kara kan hukuncin da aka yanke mishi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A makon da ya wuce ne aka yanke wa Claudio Sciarpelletti, hukuncin daurin jeka-ka-gyara-halin-ka, na watanni biyu, saboda samun shi da laifin taimakawa, wajen aikata laifi.
Hukuncin na zuwa ne, ‘yan makwanni, bayan da aka yanke wa mai kula da ma’aikatan fadar ta Paparoma, Paolo Gabriele hukuncin daurin watanni 18, saboda samun shi da laifin fidda wasu bayan sirri, da yace yana kokarin kawo karshen aikata laifuka ne a fadar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu