Isa ga babban shafi
Turai

zanga zangar tsadar rayuwa ta barke awasu kasashen Turai

Ma’aikata a daukacin kasashen dake yankin kudancin Turai, a yau sun gudanar da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa, abinda ya gurgunta harkokin yau da kullum, da kum hana jirage sama guda 700 tashi.

Masu zanga zanga a Madrid na Espaniya 14 novembre 2012.
Masu zanga zanga a Madrid na Espaniya 14 novembre 2012. AFP PHOTO/DANI POZO
Talla

Su dai shugabanin ma’aikatan sun yi kira yajin aikin ne, ganin yadda gwamnatocin kasahsensu ke cigaba da daukar matakan tsuke bakin aljihu kala kala, wadanda ke shafar rayuwar su.

Rahotanni sun ce, yajin aikin da kuma zanga zangar, sun samu karbuwa a kasashen Spain da Portugal, wanda shine irin sa na farko, kamar yadda aka samu a kasar Girka.

Kungiyar ma’aikatan kasashen Turai, wace itace ta shirya zanga zangar goyan bayan, tace a wannan karon ne aka samu hadin kai gaba daya, wajen gudanar da zanga zangar ta bai daya.

Sakatare Janar na kungiyar, Bernadette Segol, yace a wasu kasashen hankali ya tashi har an samu arangama da Yan Sanda, inda ya bukaci daukar matakan da zasu magance matsalar tattalin arzikin da Yankin ke fuskanta.

Ignacio Fernandez Toxo, daya daga cikin wadanda suka shirya zanga zangar, yace sun dauki matakin ne dan kafa tarihin gwagwarmayar yan kwadago a Turai.

A Madrid Yan Sanda sun sanya shinge tsakanin masu zanga zangar da Majalisar kasar, a kasar Portugal an ce kashi 90 na ma’aikatar kasar sun shiga wannan zanga zanga.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.