Isa ga babban shafi
Myanmar-Faransa

Suu Kyi ta gana da Hollande a Paris

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande yace Faransa za ta taimaka ga ci gaban Demokradiyar kasar Myanmar bayan ya gana da shugabar Adawar kasar Aung San Suu Kyi da ke kammala Ziyara a kasashen Turai.

Shugaban kasar Faransa François Hollande a lokacin da yake ganawa da Aung San Suu Kyi Shugabar Adawar kasar Myanmar a ziyararta ta kwanaki uku a Faransa
Shugaban kasar Faransa François Hollande a lokacin da yake ganawa da Aung San Suu Kyi Shugabar Adawar kasar Myanmar a ziyararta ta kwanaki uku a Faransa /Gonzalo Fuentes
Talla

Aung Sann Suu Kyi, jagorar fafutukan kafa mulkin democradiyyar a kasar Myanmar, ta kwashe kwanaki tana shawagi a kasashen Turai.

Sai dai Suu Kyi ta yi kiran zuba hannun jari a Myanmar domin ci gaban tattalin arzikin kasar da ke tangal-tangal.
Uwargida Aung San Suu Kyi za ta kwashe kwanaki Uku a faransa inda zata gana da kusoshin Gwamnati da kungiyoyin kare hakkin Bil’adama da kuma ‘Yan kasar Myanmar mazauna Faransa.

Suu Kyi mai shekaru 67 na haihuwa a Bara ne aka sake ta daga daurin talala a gidan yari bayan ta kwashe shekaru sama da 20 a daure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.