Isa ga babban shafi
Faransa-Italiya

Ziyarar Hollande a kasar Italia

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande zai gana da takwaransa, Mario Monti na Italia a ziyarar farko da zai kai Birnin Rome a matsayin shugaban kasa. Ziyarar Hollande na zuwa ne a dai dai lokacin da kasar Italiya ke kokarin kaucewa fadawa cikin kasashen da suka tsunduma a matsalar bashin kasashen Turai.

Fira Ministan Italiya Mario Monti a lokacin da ya ke ganawa da  shugaban Faransa François Hollande, a Birnin Bruxelas
Fira Ministan Italiya Mario Monti a lokacin da ya ke ganawa da shugaban Faransa François Hollande, a Birnin Bruxelas REUTERS/Michel Euler/Pool
Talla

Ana tunanin Tattaunawa shugabannin biyu, za ta karkata ne akan batun samar da ci gaba hanyoyin warware matsalar bashin kasashen Turai.

Ganawar hollande da Monti mabude ne ga taron da kasashen Italiya da Faransa da Jamus da kuma Spain za su yi a ranar 22 ga watan Yuli.

A karshen watan Juni ne kasashen Turai zasu gudanar taro a birnin Brussels.

Kamfanin Dillacin labaran Faransa ya rawaito cewa a wata tattaunawa da shugabannin biyu su ka yi a watan jiya a Camp David, shugabannin sun nuna sha’awar yin aiki tare domin shawo kan matsalar biyan basussuka da ke addabar kasashen Nahiyar Turai.

Masana tattalin arziki sun bayyana cewa, dole ne shugaba Monti ya yi hanzari wajen ganin ya shawo matsalar dimbin bashin da ke kan kasar Italiya domin kaucewa shiga halin ha’ula’i.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.