Hollande da Merkel sun yi alkawalin yin aiki tare don ci gaban Turai
Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande, tare da takwararsa ta kasar Jamus, Angela Merkel, sun yi alkawarin aiki tare, don ganin sun magance matsalolin da ke addabar kudin euro da kuma tattalin arzikin Turai.
Wallafawa ranar:
Bayan ganawar da suka yi ta farko a Berlin, jim kadan bayan rantsar da sabon shugaban, shugabanin biyu sun tattauna kan banbancin ra’ayin da ke tsakaninsu.
Wannan ita ce ziyarar Francois Hollande ta farko a matsayin Shugaban kasar Faransa.
An dai yi has ashe za’a tashi baran-baran tsakanin shugabannin biyu saboda sabanin ra’ayi game da matsalar tattalin arzikin Turai amma a lokacin da suke ganawa shugabannin sun yi kokarin hada kai domin samun daidaito.
A lokacin da yake jawabi, Hollande yace Jamus da Faransa zasu hada kai domin samar da ci gaba a Nahiyar Turai.
Shugabannin biyu sun bayyana fatansu wajen ganin dorewar kasar Girka a kungiyar kasashe masu amfani da kudin euro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu