Takaddama ta kaure a Jamus bayan wasu sun yi kokarin raba Qur’ani
Hukumomin Kasar Jamus sun nuna damuwarsu game da yadda wata kungiyar addinin Islama ke yunkurin raba kur’ani Miliyan 25 ga jama’ar kasar Abinda gwamnati tace cin zarafin littafi mai Tsarki ne.
Wallafawa ranar:
Shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi Allah waddai da wannan yunkuri na raba Al Qur’ani mai girma wanda aka rubuta cikin harshen Jamusanci.
Wannan al’amarin ya janyo Muhawara tsakanin ‘Yan siyasan kasar.
Sai dai masu raba Qur’anin suna ganin ya kamata a girmama ‘Yancin addini a kasar.
Kodayake wasu kungiyoyin addinin Islama sun soki wanan yunkuri da yan salafiya ke kokarin yi abinda yasa gwamnatin kasar son sanin inda kudin raba Al Qur’ani ya fito.
Kungiyar salafiyya masu ikirarin addinin gaskiya sun sha alwashin raba Al Qaur’ani ne a kan titunan kasashen Jamus, Austria, Switzerland tare da watsa wasu a Intanet don cim ma manufarsu na musuluntar Jama’a, abinda gwamnati ta kira hanyar haifar da jahadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu