Isa ga babban shafi
IMF-Turai

Kasashen Turai sun amince da bukatar IMF

Kasashen Turai 17 masu amfani da kudaden Euro sun amince su bada kudaden da suka kai Euro miliyan 150 ga Asusun Bada Lamuni, IMF, domin amfani da kudaden wajen farfado da darajar Kudin Euro. Kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP yace ya samu tabbacin amincewar kasashen kan kudirin.

Kudin Euro da kaashen Turai 17 ke amfani dasu a kasashensu
Kudin Euro da kaashen Turai 17 ke amfani dasu a kasashensu Reuters/Yves Herman
Talla

Kafar na cewa manufar wannan shi ne a samu kudin da ya kai Euro miliyan 200, kamar yadda Shugabannin kasashen Turai suka tsayar da shawara a taronsu na ranar 9 ga watan Disemba da suka gudanar, duk da cewa kasar Birtaniya na ja da baya game da bukatar samar da kudi kusan Euro biliyan 30 karkashin bukatar Asusun Bada Lamuni na duniya, IMF.

Bayanan na cewa sauran kasashen Kungiyar Turai zasu kare matsayinsu, duk da cewa sun amince da adadin kudaden da ake bukata daga manyan kasashe 20, masu karfin tattalin arziki na duniya.

Majiyoyin na cewa Ministan Kudi na kasar Birtaniya George Osborne, a wani taro ya shimfida wasu ka’idojin na bada duk wani tallafi, domin yana ganin Baitulmalin Gwamnati ba zatu rika bada gudunmawa ba ga abinda ya shafi kasashe masu amfani da kudaden Euro ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.