An Nada Sabon Shugaban Bankin Nahiyar Turai
Kungiyar tarayyar turai ta nada dan kasar Italiyar nan Mario Draghi, a matsayin shugaban babban bankin nahiyar Turai, BCE, jami’in da ya kasance kwarare wanda kuma ya sha samun lambobin yabo a kasashen duniya, zai tunkari matsalolin bashin da suka yiwa nahiyar ta turai katutu ne. Dan shekaru 63 a duniya Mr Mario Draghi, zai gaji mai barin gadon shugabancin Bankin ne, dan kasar Fransa Jean-Claude Trichet, da zai tattara yan komatsansa a ranar 1 ga watan November wannan shekara ta 2011Nadi na Mista Mario Draghi ya zo ne a dai dai lokaci da kasar Girka ke cikin halin matsin tattalin ariziki, inda a yau kasashen na Turai, suka bayyana aniyarsu na kara tallafa mata, amma kuma, sai in ta cika sharuddan tsuke bakin aljihun gwamnatin da suka gindaya mata.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: