Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha zata amince ga shiga tsakanin rikicin Libya

Gwamnatin kasar Rasha tace zata amince ga shiga tsakanin rikicin Libya bayan da takwarorinta suka bukaci kasar da yin haka a taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G8. A cewar mataimakin Ministan harakokin wajen kasar Sergei Ryabkov, wannan wata dama ce ga kasar Rasha na kawo karshen rikin kasar Libya idan dai har zata ci gaba da tattaunawa da hukomomin libya da hakan kuma zai sa Gaddafi ya dauki matakin da ya dace.Sai dai Mista Ryabkov yace Gaddafi ya saba ka’ida kuma ya dace ace ya yi bankwana da mukaminsa, amma Rasha zata taimaka masa idan har ya bukaci neman mafaka.Kasashen na G8 dai na ganin cewa kasar Rasha zata taka muhimmiyar rawa musamman kawancenta da Libya kodayake wasu suna ganin huldar kasar da Libya ba a bayyane bane. 

Shugaban kasar Rasha Dmitri Medvedev a taron kasashen G8 dake gudana a kasar Faransa.
Shugaban kasar Rasha Dmitri Medvedev a taron kasashen G8 dake gudana a kasar Faransa. REUTERS/Alexander Natruskin
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.