Isa ga babban shafi
Turai

Ministan Kudin Faransa Lagarde ta bayyana neman shugabantar IMF

Ministan Kudin kasar Faransa, Christian Lagarde, ta sanar da takarar ta na neman shugabancin Hukumar Bada Lamini ta duniya, a daidai lokacin da kasashe masu tasowa ke neman sauyi.Bayan an dade ana ta rade radi, yanzu ta tabbata cewar, Christine Lagarde, Ministan kudin Faransa, zata tsaya takarar shugabancin Hukumar Bada Lamini ta duniya, IMF, sakamakon murabus din Dominique Strauss Kahn.Lagarde mai shekaru 55 da haihuwa, idan ta samu nasarar samu aikin, zata zama mace ta farko da zata shugabanci Hukumar ta IMF.Ministan, wanda lauya ce a kasar Amurka, ta koma gida a shekara ta 2005, inda ta zama Ministan kasuwanci a karkashin Gwamnatin Jacques Chirac, yayin da shugaba Nicolas Sarkozy, ya nada ta Ministan noma cikin shekara ta 2007, kuma ya maida ita ministan kudi daga bisani.Shugaban kungiyar kasashen Turai, Jose Manuel Barosso, ya ce Lagarde na da duk wata kwarewa da ake bukata na samun wannan kujera.Tuni dai kasashe da dama suka bayyana goyan bayan ta, na ganin ta samu mikamin, cikinsu harda Jamus, Birtania, Italiya, Amurka da China, yayin da kasashe masu tasowa irinsu Brazil, China, Russia, Indiya da Afrika ta kudu, ke neman ganin an daina maida aikin mallakar kasahsen Turai kawai.

Ministan Kudin Kasar Faransa Christine Lagarde
Ministan Kudin Kasar Faransa Christine Lagarde Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.