Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta yi waje da jami’an Libya 14

Gwamnatin kasar Faransa ta gargadi wasu jami’an huldar diplomasiyar kasar Libya 14 bisa zarginsu da biyayya ga gwamnatin shugaba Muammar Gaddafi, kamar yadda ma’aikatar harakokin wajen kasar ta sanar.Wani jami’in diplomasiyar kasar Faransa ya shaidawa manema labarai cewa a dazun nan ne suka yanke wannan hukuncin sai dai akwai matakan da zasu bi domin tabbatar da haka.A yanzu haka dai kasar Birtaniya da Faransa suna kokarin hada damtse da kungiyar NATO/OTAN domin karya dakarun shugaban Libya Mu’ammar Gaddafi a matakin Majalisar Dunkin Duniya na kare rayukan fararen hula a Libya.Kasar Faransa ta kayyade tsakanin awanni 24 zuwa 48 ga jami’an kasar ta libya da su fice daga kasar 

Ministan Harakokin Wajen kasar Faransa, Bernard Kouchner,
Ministan Harakokin Wajen kasar Faransa, Bernard Kouchner, AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.