Isa ga babban shafi
Ukraine

‘Yan majalisar kasar Ukrain sun ba hamata iska

Masu gabatar da kara a kasar Ukrain a yau Juma’a zasu bude littafin binciken wasu ‘yan majalisun kasar Ukrain da suka ba hamata iska a zauren majalisar. Rikicin ‘yan majalisun wanda ya faru tsakanin ‘yan Jam’iyyar  Tymoshenko's BYuT-Batkivshchyna da kuma Jam’iyyar Shugaba Viktor Yanukovych, ya yi muni matuka wanda ya yi sanadiyar kwantar da ‘yan majalisu uku a gadon asibiti.Mataimakin madugun jam’iyyun adawa Mykhailo Volynets, jina-jina dai aka dauke shi daga zauren majalisar tare da mabiyansa Volodymyr Bondarenko da Yuriy Gnatkevych.A yanzu haka masu gabatar da kara sun bayyana gudanar da kwakkwaran bincike ba tare nuna fifiko ba ga wani bangare, kamar yadda babban mai gabatar da kara a kasar Viktor Pshonka ya shaidawa manema labarai.Rehotanni na nuna cewa ‘yan adawa ne suka kargame kansu a cikin zauren majalisar tare da lika wasu takardun na nuna kyama ga Tymoshenko wanda ya kuma hakan ya haddasa rikicin. 

Yulia Tymoshenko yayin da take ganawa da manema laba lokacin da takai ziyara ofishin masu gabatar da kara a  Kiev
Yulia Tymoshenko yayin da take ganawa da manema laba lokacin da takai ziyara ofishin masu gabatar da kara a Kiev Reuters/Alexander Prokopenko/Yulia Tymoshenko Press Service
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.