Isa ga babban shafi
Greece-EU-IMF

An Warware Matsalar Kudi Na Girka

Kasashen Turai tare da Asusun Bada Lamuni na Duniya sun cimma matsaya na bada kudaden agaji daya kai Euro biliyan 750 ga kasar Girka.    A yanzu ke nan ana saran kawo karshen rigingimun kasar gameda batun komadan tattalin arziki.Shugabannin kasashen Turai na fatan rancen zai hana kudin Euro fuskantar matsala daga matsalolin kudi daya afkawa kasar ta Girka, dake barazanar bazuwa kasashen Spain da Portugal.Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fadawa manema labarai cewa wannan rance ga kasar Girka zai taimaka da kara karfi kudin na Euro.Wannan tallafin kudi dai ya kunshi Kudin Euro biliyan 440 daga kasashe 16 dake amfanio da kudin Euro, da kuma Euro biliyan 60 daga Hukumar kasashen Turai da kuma Euro biliyan 250 daga Asusu bada lamuni na Duniya.  

rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.