Isa ga babban shafi
Girka- IMF

Matsalar Kudin Girka Na Barazana Ga Kasashen Turai

Shugaban Asusun bada lamuni na Duniya Dominique Strauss-Kahn, yayi gargadin cewa matsalar tattalin arzikin kasashen Turai masu amfani da kudin Euro na cikin hatsari sakamakon matsalolin da aka samu na kasar Spain da kuma batun baiwa kasar Girka kudin daya kai Euro billiyan 120.Shugaban na magana ne a Berlin na Jamus  lokacin daya kai ziyara domin neman goyon bayan kasar saboda batun bada tallafin ga kasar Girka domin ta fita daga cikin matsalolin da take fama.Dominique Strass-Kahn na mai fargaban cewa lamarin kasar Girka na iya shafan sauran kasashen Turai.Prime Ministan kasar Girka, George Papandreou ya fadi cewa Kungiyar Tarayyar Turai dole ne tayi wani abu domin kaucewa masifan dake tafe.Shugaban kasar Faransa Barack Obama, ajiya, ya nemi Shugaban Gwamnatin kasar Germus, Angela Merkel, sun nuna muhimmancin agazawa kasar Girka domin ta shawo kan matsalar komadan tattalin arziki daya afka mata.  

rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.