Isa ga babban shafi

Afrika ta Tsakiya za ta fara cin Bitcoin a hukumance

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a hukumance ta amince da kudin internet na bitcoin, inda ta zama kasa ta biyu a duniya da ta yi hakan bayan El Salvador.

Représentation des monnaies virtuelles Bitcoin, Ethereum, DogeCoin, Ripple et Litecoin.
Représentation des monnaies virtuelles Bitcoin, Ethereum, DogeCoin, Ripple et Litecoin. © REUTERS - Dado Ruvic
Talla

'Yan majalisa dokokin kasar suka amince da kudirin da shugaban kasar Faustin Archange Touadera.

ya gabatar musu da gagarumin rinjaye, lamarin da ya sa yanzu Bitcoin ya zama daya daga cikin kudi da kasar zata yi amfani da su a bangaren CEFA tare da halatta amfani da cryptocurrencies.

Tuni shugaba Touadera ya sanya hannu kan matakin da yanzu ya zama doka, kamar yadda shugaban ma’aikantan fadar shugaban kasar Obed Namsio ya sanar

Yanzu haka dai CAR "ita ce kasa ta farko a Afirka da ta amince da kudin na yanar gizo mai daraja, wanda ake canja kwaya daya kan kudi sama da Naira miliyan 16, duk da cewa wasu kasashe irinsu da Najeriya sun haramta amfani da kudaden na Crypto ciki harda Bitcoin, saboda fargabar saukinsu wajen halasta kudaden haramun ko taimakawa ta’addanci.

Saboda miyagu na iya samun kudin cikin sauki ba tare da bankuna sun sanya ido ba.

‘Yan adawan kasar sun yi Allah wadai ta matakin da suka kira shirin shugaba Faustin Archange Touadera na watsi da kudin CEFA saboda alakarsa da kasar Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.