Isa ga babban shafi
Amurka-China

Arzikin Amurka da China na bunkasa cikin sauri- IMF

Asusun Bada Lamuni na duniya IMF ya ce, tattalin arzikin kasahen Amurka da China na habbaka cikin hanzari duk kuwa da yadda ake kokawa game da durkushewar tattalin arzikin a sassan duniya.

 Shugabar Asusun IMF Kristalina Georgieva i
Shugabar Asusun IMF Kristalina Georgieva i AFP/File
Talla

Shugabar Asusun Kristalina Georgieva ce ta bayyana hakan, tana mai cewa cikin watan Janairu sun yi kiyasin faduwar tattalin arzikin duniya da kashi biyar da rabi cikin dari, kuma akwai hadari kafin a dawo yadda ake a baya.

Sai dai ga mamakinsu a cewar Kristalina, tattalin arzikin kasashen biyu na habbaka cikin sauri tun farkon shekarar nan zuwa yanzu.

Ta ce,  a yadda abubuwa ke tafiya, akwai kyakkyawan zaton cewa tattalin arzikin kasashen biyu zai kara habbaka fiye da yadda yake a yanzu nan ba da jimawa ba.

A cewarta, sirrin habbakar tattalin arzikin Amurka, na da nasaba da shirin sabon shugaba Joe Biden na ware Dala tiriliyan tara da biliyan dari tara don raba wa mutane, a wani yunkuri na rage musu radadin da cutar annobar corona ta zo da shi.

Wanda ta ce hakan ya haifar da jujjuyawar kudade a hannun mutane, kuma da ma hakan sirrin habbakar tattalin arziki ne.

Baya ga wannan kuma, ta ce akwai irin gwaggwaban tallafin da ake bai wa likitoci da masu aikin jinya, musamman wadanda ke kula da masu fama da annobar corona.

Ta kuma kara da cewa, habbakar tattalin arzikin kasashen ba iya su ya shafa ba, don kuwa da tattalin arzikin na su bai habbaka ba, za a samu mummunar faduwar tattalin arziki, da za ta shafi kowacce kasa a duniya.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.