Isa ga babban shafi
Wasanni

Gudunmawar Marigayi Isma'ila Mabo ga bangaren wasannin Najeriya

Wallafawa ranar:

A farkon wannan watan na Maris ne, Nigeria ta rasa daya daga cikin zakakuran tsaffin ‘yan wasan kwallon kafa na kasar, Sama’ila Mabo, bayan jinyar da ya sha fama da ita a garin Jos, babban birnin jihar Plateau, wannan shi ne maudu'in da shirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali akai.

Mai horarwa Isma'ila Mabo tare da editan sashen Hausa na RFI Bashir Ibrahimm Idris.
Mai horarwa Isma'ila Mabo tare da editan sashen Hausa na RFI Bashir Ibrahimm Idris. © RFI HAUSA
Talla

An dai haifi marigayi Sama’ila Mabo, a ranar 15 ga watan Yulin shekarar 1944 a garin Jos, kuma ya koma ga mahaliccinsa yana da shekaru 78. 

Kafin rasuwarsa, marigayi Sama’ila Mabo, ya jagoranci Club din Kwallon Kafa na mata na Nigeria wato Super Falcons a matsayin Kochi, inda suka fafata a gasar cin kofin duniya ta mata a shekarar 1999, sannan ya kai su gasar wasannin Olympics ta 2000 da kuma wacce aka yi a 2004. 

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.