Akwai yuyuwar samun ambaliyar ruwa a Najeriya a daminar bana-NIMET
Wallafawa ranar:
Kunna - 19:54
Hukumar kula da hasashen yanayi ta tarayyar Nigeria NIMET, ta ankarar da mazauna wasu jihohin arewacin kasar dangane da mamakon ruwan saman da ake sa-ran zubawa nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
A cewar hukumar, wacce kan yi hasashen yadda yanayi zai kasance a kasar, tuni na’urorinta suka hango alamomin tsawa da walkiya a yankunan jihohin Borno, Taraba, Gombe, Bauchi da kuma Kano.
Wannan hasashe na zuwa ne yayinda har yanzu, wasu al’ummomin kasar, ba su gama farfadowa daga barnar da ambaliya ta yi musu a daminar bara ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu