Isa ga babban shafi
Masarautunmu

A Najeriya yan bindiga sun sako sarkin Gindiri a Jihar Plateau

Wallafawa ranar:

A Najeriya, bayan share tsawon kwanaki 5 a hannun masu garkuwa da shi, a sanyin safiyar yau juma’a basaraken gargajiya na masarautar Gindiri a jihar Plateau Mai Martaba Charles Mato Dakat, ya kubuta inda ya koma a cikin iyalansa.Da farko dai an ruwaito cewa wadanda suka yi garkuwa da basaraken sun bukaci a biya milyan 50 a matsayin kudin fansa kafin su sake shi, to amma makusantan sarkin sun ce ba a biya ko sisin kobo ba. Daga Jos, ga rahoton da Tasiu Zakari ya aiko mana.

'Yan bindiga sun addabi jihar Plateau a Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Plateau a Najeriya © dailypost
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.