Isa ga babban shafi
Ilimi Hasken Rayuwa

Najeriya za ta fara kwashe daliban kasarta da ke Sudan zuwa Masar

Wallafawa ranar:

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce sun fara tattaunawa da mahukuntan kasar Masar a birnin Alkahira, kan yadda za a kwaso daliban kasar daga Sudan, yayin da bangarori biyu ke ci gaba da gwabza yaki a kasar da ke Gabashin Afirka.

Yadda dakarun gwamnati ke aikin sintiri a birnin Khartoum na kassar Sudan.
Yadda dakarun gwamnati ke aikin sintiri a birnin Khartoum na kassar Sudan. Reuters
Talla

Wannan ya zo ne, bayan da dubban dalibai 'yan Najeriyar da ke karatu a Sudan suka mika koken su ga gwamnatin kasar, game da mummunan yanayin da suke ciki, saboda tashe-tashen hankula a Khartoum, babban birnin ƙasar.

Sojojin gwamnati da kuma dakarun RSF sun shafe sama da mako guda suna rikici da juna, lamarin da ya jefa fararen hula da dama cikin mummunan yanayi.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin da Shamsiyya Haruna ta gabatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.