Kamala Harris ta sanar da tallafin dala miliyan 139 da Amurka ta ba Ghana
Wallafawa ranar:
Kunna - 02:54
Amurka ta sanar da tallafin dala milyan 139 ga kasar Ghana, domin kyautata tsaro, tattalin arziki da kuma samar da ci gaba, kamar dai yadda aka sanar jim kadan bayan ganawar da aka yi tsakanin shugaban Ghana Nana Akufo-Addo da mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris a birnin Accra.
Ghana dai, ta kasance a ziyarar da Harris za ta kai a kasashe uku na Afirka, kuma zantawarsu da wakilinmu Abdallah Sham’un Bako, masani harkokin diflomasiyya Adib Sani da ke zaune a birnin Accra, ya bayyana wasu daga cikin dalilan da suka sa Amurka ke kara zawarcin nahiyar Afirka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu