Isa ga babban shafi
NIJAR-SIYASA

Bazoum ya gana da Magadan Gari akan ayyukan raya kasa

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya gana da Magadan Gari da shugabannin kananan hukumomi da kuma Kantomomi inda ya jaddada musu muhimmancin gudanar da ayyukan raya kasa da kuma inganta yankunan su.

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed na ganawa da Magadan Gari
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed na ganawa da Magadan Gari © Niger Presidency
Talla

Mohammed ya tabo yadda Nijar ta kaddamar da shirin gudanar da ayyukan yankuna a shekarar 2004 amma kuma ba’a sabunta su ba tun da aka kirkiro su a shekarar 2011, inda yake cewa ba zasu bari a bata lokaci wajen inganta su ba.

Shugaban ya bayyana cewar Hukumar zaben kasar CENI zata ci gaba da gudanar da ayyukan ta kamar yadda ta saba da kuma gudanar da zabuka kamar yadda doka ta tanada.

Tawagar Magadan Garin Nijar
Tawagar Magadan Garin Nijar © Niger Presidency

Mohammed ya bayyana fatar ganin an gudanar da zaben kananan hukumomi kafin na Yan Majalisu da kuma na shugaban kasa.

Shugaban ya danganta matsalolin da ake samu wajen tafiyar da kananan hukumomi da rashin fahimta daga jami’an su, inda ya jaddada muhimmancin samun horo domin kaucewa tafka kuskure.

Mohammed ya jaddada muhimmancin baiwa kananan hukumomin dama wajen fahimtar dokokin da aka tanada domin tafiyar da su, yayin da ya bukaci shugabannin da su mayar da hankali wajen daukar kwararrun ma’aikata.

Shugaban ya kuma bayyana dalilin da ya mika harkokin sayar da abinci ga jama’a a farashi mai sauki ga Kantomomi maimakon Magadan Gari sakamakon matsalolin da aka samu a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.